Siriya: Su wa ke fada da juna?
Yakin Siriya ya barke ne a yayin da guguwar sauyi ta kada a yankin Gabas ta Tsakiya a shekarar 2011, rikicin ya haifar da rabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya da ke mara wa bangaren da suke so baya.
Yakin da ya ki ci ya ki cinyewa
Yakin basasa ya barke a Siriya tun daga shekarar 2011 bayan da Shugaba Bashar Assad ya rasa karfin iko na akasarin kasar, yankuna sun koma karkashin ikon 'yan tawaye. Rikicin ya ci gaba da haifar da sabani a tsakanin kasashen duniya, baya ga jefa al'ummar kasar cikin kunci tare da lakume rayukan dubbai na mutane.
Mai mulkin kama karya
Rundunar sojin Siriya da aka fi sani da Syrian Arab Army (SAA), ta bayar da goyon baya dari bisa dari ga Shugaba Bashar al-Assad, a kokarin ganin ya kwato ikon yankunan da suka kubuce masa tare da ci gaba da shugabancin kasar. Rundunar ta ci gaba da yakar abokan gaba bisa taimakon Rasha da Iran da ke son ganin ya ci gaba da mulki.
Mai sa ido daga arewaci
Turkiyya na daga cikin rundunar kawance da Amirka ke jagoranta. Ta ci gaba da mara wa 'yan tawaye da ke yakar bangaren Assad baya. Sai dai akwai dan tsamin dangantaka a tsakaninta da Amirka kan yadda take taimaka ma 'yan tawayen Kurdawa da ake alakantawa da mayakan kungiyar PKK. Sau uku rundunar sojin Ankarar ta kaddamar da farmaki kan 'yan tawayen Kurdawan a Siriya a cikin shekaru uku.
Kulawa daga yankin gabashin duniya
Gwamnatin Kremlin ta kasance aminiyar Assad. Sojojin kasar na sama da na kasa sun shiga yakin a shekarar 2015 bayan da suka dade suna taimaka mata da makamai. Rasha ta fuskanci tsananin suka saboda hakan daga manyan kasashen duniya inda aka zarge ta da hannu a mutuwar daruruwan fararen hula a yayin hare-haren kan abokan gabar Assad. Sai dai duk da haka shiga yakin ya bai wa Assad nasara.
Aminai na kasashen yamma
Amirka ta jagoranci rundunar kawance na kasashen duniya fiye da 50, ciki har da Jamus da zummar karya lagon kungiyar IS. Ta kai hare-hare ba kakkautawa. Rundunar kawance ta yi tasiri kan mayakan. Amirka na da sama da sojoji 1000 da ke mara wa rundunar 'yan tawaye ta Syrian Democratic Forces ko SDF.
'Yan tawaye
'Yan tawayen Syrian Army sun kafu ne bayan da suka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Assad, kafin ta rikide zuwa tarzoma. Da goyon bayan wasu kungiyoyin 'yan tawaye suka nemi tumbuke gwamnatin don samar da mulki karkashin tsari irin na dimukuradiyya. Hakarsu ba ta cimma ruwa ba, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu sauya sheka. Duk da goyon bayan Amirka da Turkiyya ba su yi nasara ba.
Turjiya
Fada a tsakanin mayakan Kurdawa da na jihadi ya kasance rikici na dabam. Rundunar kawancen da Amirka ke jagoranta da ke yakar IS ta kuma bai wa mayakan na Syrian Democratic Forces goyon baya. SDF ta kunshi mayakan Kurdawa wadanda suka kasance kashin bayan gamaiyar.
Bullar mayakan jihadi
Kungiyar IS ta yi amfani da tashin hankali a Siriya wajen samun kafar shiga Iraki inda ta yi nasarar karbe akasarin ikon manyan birane a shekarar 2014. Kungiyar da ke da'awar jihadi tare da son kafa daular Islama, ta yi bakin jini, inda take shan tofin alla tsine kan bata wa addinin Musulunci suna. Yanzu kungiyar na gab da faduwa a sakamakon farmakin da Amirka da Rasha suka kaddamar kanta.
Tsoffin mayakan jihadi
Ba kungiyar IS ce kadai ta haddasa barna a yakin Siriya ba, akwai mayaka na kungiyoyi dabam-dabam da ke fada a rikicin, akwai masu adawa da wasu kungiyoyi da kuma wadanda ke adawa da gwamnatin Assad. Daga ciki akwai kungiyar Hay'at Tahrir al-Sham, da ke da karfin iko a akasarin biranen da ke karkashin yankin Idlib. Kungiyar na da alaka da al-Qaeda.
Yankin Pasha
Iran ta dade tana goyon bayan Siriya kuma ta ci gaba da rike wannan dangantaka da muhimmanci. Gwamnatin Tehran ta taimaka wa gwamnatin Damascus da dabarun yaki, ta horas da mayakanta tun daga lokacin da rikicin ya barke a shekara ta 2011. Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanan ita ma ta mara wa Assad baya, inda suke yi wa abokan gaba taron dangi.