Siriya ta mayar da martani ga Erdogan
December 27, 2017Talla
Ma'aikatar harkokin kasashen ketaren ta Siriya dai, na mayar da martani ne ga Shugaba Erdogan bisa kalamansa na ayyana shugaban kasar Siriyan Bashar al-Assad a matsayin dan ta'adda. Erdogan ya ce ba ya jin zai iya ci gaba da tattauna batun rikicin Siriyan da Shugaba Bashar al-Assad wanda ya ce ya yi ta'addanci a kan al'ummarsa. Shugaban na Turkiyya ya bayana hakan ne a jawabin da ya yi ga manema labarai a Tunusiya yayin ziyarar aiki da yake a kasar. Kalaman na Erdogan dai su ne mafi zafi da ya yi a kan Assad a dai-dai lokacin da kasashen Turkiyya da Rasha da kuma Iran ke kokarin ganin sun shawo kan rikicin na Siriya da ya lakume rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.