Siriya ta tsira daga takunkumi
February 28, 2017Talla
Daman dai kasashen Birtaniya da Faransa da kasar Amirka ne ke kan gaba wajen ganin hakar su ta cimma kuri'ar sanya wa gwamnatin Siriya takunkumin, bisa zargin ta da amfanin da makamai masu guba a yakin da ta ke yi da 'yan 'yan tawaye.
Kwamitin na Majalisar Dinkin Duniya na bukatar kuri'u na akalla kashi tara da ke goyon bayan kudirin, kan a amince da zartas da ko wani mataki. Wannan dai shi ne karo na bakwai da kasar Rasha ke amfani da karfin ikonta na marawa Siriya baya, sai kuma a wannan karon da ta samu hadewar kasar China.
Ana dai dab da sanya sunayen wasu kwamandojin Siriya 11, dama kasar baki daya cikin jerin kasahen da ke amfani da makamai masu guba, amma dai gwamnatin Bashar al-Assad ta sha musanta wannan zargi.