1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta zargi rundunar kawance da kashe mata sojoji

Gazali Abdou TasawaDecember 7, 2015

Siriya ta zargi rundunar kawancan kasashen duniya mai yaki da Kungiyar IS da kai hari a kan barikin sojin gwamnatin kasar ta Deir Ezzor da ke a Gabashin kasar tare da hallaka uku daga cikinsu a jiya Lahadi.

https://p.dw.com/p/1HIlC
Frankreich Luftwaffe Kampfjets
Hoto: picture alliance/dpa/Ecpad Handout

Kasar Siriya ta zargi rundunar kawancan kasashen duniya mai yaki da Kungiyar IS da kai hari a kan wata barikin sojoji gwamnatin kasar da ke a garin Deir Ezzor na Gabashin kasar tare da hallaka uku a jiya Lahadi.

Ministan harakokin wajen kasar ta Siriya wanda ya bayyana rashin amincewarsa da harin wanda ya bayyana shi da keta haddin dokokin Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta daukar mataki na ganin irin wannan hadari bai sake abkuwa ba.

Sai dai rundunar kawancen da Amirka ke jagoranta ta bakin kakakinta Kanal Steve Warren ta musanta zargin kai harin kan sojin gwamnatin Siriyar.

Sai dai daga nata bangare babbar kungiyar kare hakin bil'adama ta kasar ta Siriya wato OSDH ta tabbatar da cewa an kai wasu hare-hare ta sama a kan wata gada da kuma wata barikin sojin gwamnati da ke a nisan kilomita biyu da birnin Ayache da ke a hannun mayakan kungiyar IS inda sojoji hudu suka mutu wasu 13 suka ji rauni.