1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: 'Yan tawaye na ficewa daga Damascus

Ramatu Garba Baba
April 21, 2018

Dubban 'yan tawaye sun zabi ficewa daga wasu garuruwa uku da ke Qalamoun a gabashin birnin Damascus bayan da suka yi sarenda ga gwamnatin kasar ta Siriya don ba ta damar yin iko da yankin.

https://p.dw.com/p/2wRS9
Syrien - Qara - Convoy aus Kämpfern und angehörigen des IS auf dem weg nach Deir al-Zour
Hoto: picture-alliance/Photoshot/A. Safarjalani

Kafafen yada labaran kasar sun rawaito yadda aka yi ta ganin ayarin motoci kirar bas bas na ficewa da daruruwan 'yan tawayen da iyalansu. Akalla 'yan tawaye 3,200 ne suka bar garuruwan a wannan Asabar ana kuma sa ran za a kwashi tsawon kwanaki uku nan gaba a wannan aiki na fitar da su kafin dakarun gwamnati su sami damar iko da yankin, a kokarin gwamnatin Bashar al-Assad na samun galaba a yakin kasar da ya dauki sama da shekaru shida ana yi.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da can kuma a kasar Sweden, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke wani taro da zummar magance rikicin kasar ta Siriya, bayan da aka zargi gwamnatin Assad da Rasha da amfani da makamai masu guba a yankin Douma inda mutane kusan 100 suka halaka, akwai wakilan kasashen duniya goma sha biyar da za su halaci zaman tare da babban magatakarda na majalisar Antonio Guterres.