Siriya: 'Yan tawaye sun amince da tsagaita wuta
February 26, 2016A lokacin da ya rage 'yan awoyi yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Siriya ta soma aiki, kungiyoyin tawaye kasar ta Siriya kimanin dari sun sanar da ba da hadin kansu ga shirin.A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Jumma'a kwamitin koli mai kula da tattaunawa wanda ya kunshi manyan kungiyoyin 'yan adawa da na 'yan tawayen Siriya ya tabbatar da wannan matsayi nasa na mutunta matakin tsagaita wutar na wa'adin makonni biyu da zai soma aiki a karfe 12 na daran wannan jumma'a.
Daga nashi bangare Shugaba Rasha Vladmir Poutin ya sanar a wannan Jumma'a cewar ko da yake babu wata hanya mafi a'ala ta kawo karshen rikicin Siriyar kamar ta sulhu amma kuma ya ce lamarin zai matukar wahala.
Sai dai kuma ya jaddada matsayinsa na ci gaba da yakar Kungiyoyin IS da na Al-Nosra wadanda matakin tsagaita wutar bai shafesu ba.