Siriya za ta bi sahu a yarjejeniyar Paris
November 7, 2017Alamu sun nunar da cewa kasar Siriya za ta bi sauran takwarorinta na duniya wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Wannan mataki dai zai sanya Amirka ta zama kasa daya tilo da ba ta cikin tafiyar da kasashen duniya suka sanya a gaba wajen cimma muradun yarjejeniyar ta Paris.
Wakilai na Siriya a taron na COP 23 da ke wakana a birnin Bonn na Tarayyar Jamus sun fada wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa kasarsu ta shirya ta sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta sanya a rage yawaitar dimamar yanayi da digiri biyu.
A cewar Sabine Minninger kwararriya kan sauyin yanayi daga masu fafutika da aikin tallafi na kungiyar Bread for the World wakilan kasar ta Siriya sun nemi a basu takardun yarjejeniyar da ake bukata da kasashe suka yi amfani da su wajen shiga yarjejeniyar.