Siriya: Zanga-zanga ta barke a Tal Abyad
October 8, 2019Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kwashe watanni yana barazanar kai farmakin soja a kan iyakar kasarsa da Siriya. Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun yi gargadin cewa kimanin mutane dubu 300 aka yi kiyasin tilas su kaurace wa gidajensu nan take, idan Turkiyyya ta kaddamar da hari a yankin arewacin Siriya da ke kan iyaka da ita. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Amirka suka fara ficewa daga yankin.
Shugaban Erdogan ya sake jaddada aniyarsa ta kai hari Siriya a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce Turkiyyya za ta kai hari ta sama da ta kasa a gabar gabashin kogin Euphrates da ke Siriya. Wannan dai shi ne karo na farko da ya kara tabbatar da aniyar Ankara ta mamaye yankin tun bayan da suka cimma yarjejeniya tare da Amirka na samar da abin da suka kira "Tudun Mun Tsira."
Erdogan dai na yi wa dakarun Kurdawan Siriya kallon 'yan ta'adda, kana barazana ga kasarsa, a daidai lokacin da Ankaran ke kokarin murkushe hare-haren sari ka noke da take fuskanta daga Kurdawan. Da yake jawabi ga magoya bayansa yayin bude taron shekara-shekara na jam'iyyarsa ta AKP Erdogan yace:-
"Mun kammala shirinmu tsaf na kai hari, mun kuma bayar da umurnin da suka dace. Lokaci ya yi da zamu share hanyar wanzuwar zaman lafiya. Za mu aiwatar da harin ta hanyar amfani da sojojinmu na sama da na kasa. Kuma ba ma tababar cewa abokanmu na Siriya za su mara mana baya da dukkanin karfinsu."
Shugaba Erdogan ya ce Turkiyya za ta yi amfani da yankin gabar kogin na Euphrates ne domin samar da tudun mun tsira ga 'yan gudun hijira. Matakin na Erdowan dai na zuwa ne bayan da shugaban Amirka Donald Trump ya bayar da umurnin janye dakarun kasarsa daga kan iyakar Siriya da Turkiyya biyo bayan tataunawa da suka yi ta wayar tarho da takwaransa na Turkiyyan.
Ba dai a birinin na Tal Abyad na Sirya ne kawai ake wannan zanga-zangar ba domin kuwa a birnin Ras al-Ayn da ke arewacin kasar ta Siriya da shi ma ke kan iyaka da Turkiyyan zanga-zangar nuna adawa da ficewar dakarun Amirka daga yankin ta barke, inda ma guda daga cikin shugabannin kwamitin shugabancin yankin Arewaci da gabashin Sirya da ke da kwarya-kwaryar 'yanci Abed Hamed al-Mihbash ke cewa:
"Muna kira ga dukkan mutanenmu na ciki da wajen kasar nan da su yi aki tukuru domin samar da wata mafita wajen dakile wannan harin na rashin adalci. Haka kuma muna kira ga jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da wadanda ke cikin Siriya su marawa dakarun gwagwarmaya baya."
A hannu guda kuma dakarun gwamnatin Siriya sun nunar da cewa a shirye suke su mayar da martani nan take, idan har Turkiyya ta yi yunkurin kai hari a kowanne yanki na kasar kamar yaddad kakakin rundunar Gabriel Keno ya nunar. Su ma dai matzauna yankin na nuna damuwarsu, inda wasu ke zargin Rasha da tallafawa kudirin na Turkiyya kan ta shiga Siriya idan Amirka ta fice daga kasar, yayin da wasunsu kuma ke fargabar halin taskun da za su tsinci kansu a ciki sakamakon harin na Turkiyya.