1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Ghana ta dauki hankalin Jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
December 13, 2024

Dawowar tsohon shugaban kasar Ghana da kuma sauyin mulki ya tabbata ne bayan da hukumar zabe a Ghana ta ayyana dan takarar adawa John Mahama a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar

https://p.dw.com/p/4o8Rm
Ghana I Wahlen
Hoto: Misper Apawu/AP/picture alliance

Frankfurter Allgermeine Zeitung wadda ta fara da cewa Dawowar tsohon shugaban kasar Ghana da kuma canjin mulki a kasar. Wannan ya tabbata bayan da hukumar zabe a Ghana ta ayyana dan takarar adawa John Mahama a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa. Wannan dai ba shi ne karon farko da ya hau mulki ba.

Tsohon shugaban kasa John Mahama ya yi murnar dawowarsa a Ghana, inda tun gabanin hukumar zabe ta ayyana wanda ya yi nasara ne dai dan takarar jam'iyya mai mulki, kuma mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye tun washegarin gudanar da zabe. Kuma hakan alama ce ta ya so ya "kauce wa tashin hankali" kamar yadda aka saba gani a sauran zabuka.

Ghana I Wahlen
Hoto: Misper Apawu/AP/picture alliance

Ita kuwa jaridar die Zeit ta duba hasarar rayuka da dukiyoyi wanda ke ci gaba da faruwa a kasar Sudan, Jaridar ta ce mutane da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamakon hare-haren da aka kai a yankunan da jama'a ke zama da kuma kasuwanni a kasar Sudan. Jaridar ta ci gaba da cewa sojoji sun kashe akalla mutane 87 tare da jikkata daruruwa a cewar hukumomi.

Yawancin wadanda suka mutu farar hula ne. Wasu munanan hare-hare da aka kai a birnin Omdurman na kasar Sudan da ke fama da yakin basasa sun kasance abu mafi zubar da jini a baya-bayan nan. A cewar gwamnatin Sudan, mayakan RSF ne ke da alhakin kai farmakin. Kuma baya ga birnin Omdurman an kai wasu jerin hare-haren a sassan kasar ta Sudan. Tun barkewar yakin basa sa a Sudan har yanzu an kasa shawo kan rikicin, sai kara lakume rayuka ya ke yi.

Wasu daga cikin Jaridun Jamus
Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jarida die tageszeitung wace ta dubi wani sabon rikicin siyasa a gabashi na mai cewa a kasar Zambia an cire sunan shugaban 'yan adawa Edgar Lungu daga ‘yan takarar zaben shugaban kasa na 2026. Kotun tsarin mulkin kasar Zambia ta fitar da tsohon shugaban kasar kuma madugun adawa a yanzu, lamarin da ya janyo cece-kuce a siyasar kasar.

A farkon wannan makon ne kotun koli ta tabbatar da karar da dan jam'iyyar UPND mai mulkin kasar ya shigar kan shugaban jam'iyyar adawa ta Patriotic Front (PF). Dama dai shi ne babban mai kalubalantar shugaba mai ci

A batun kiwon lafiya za mu duba sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung , inda ta ce a hirar da aka yi da masana, yawaitar barkewar cututtuka a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango abin tada hankali ne, kuma a zahiri kasar na bukatar sauya matakan kiwon lafiya. A kwannanan ne dai wata cutar da ba a gano ko wace iri ce ba, ta bulla a Kwango kuma ta na hallaka mutane.

Kula da lafiya a JAmhuriyar Dimukuradiyyar Kongo
Kula da lafiya a JAmhuriyar Dimukuradiyyar KongoHoto: Makangara Ciribagula Justin/Anadolu/picture alliance

Bayan jinkirin da hukumomin yankin da cutar ta bulla suka yi game da mace-macen da ke faruwa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, wani masanin cututtuka na a kasar Jamus ya yi kira ga daukacin kasashen duniya a taya Kwango a dauki matakin gaggawa kan irin wannan cutar. Dole ne a gano barkewar cututtuka da kyau kuma a iya magance su ko da a cikin yankuna masu nisa ne, in ji Torsten, Feldt, Mukaddasin shugaban Likitoci Jamusawa masana cututtukan da ke samuwa a wurare masu zafi na duniya, 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani