1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Kenya da rikicin Bangui a Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal ARH
September 1, 2017

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da tasirin wasan kwalon kafa kan tashe-tashen hankula a Kenya, da tsokaci kan taron Paris kan 'yan gudun hijira sun dauki hankalin jaridun Jamus a nahiyar Afirka a mako mai karewa.

https://p.dw.com/p/2jDkS
Kenia Wahlen Uhuru Kenyatta
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokaci kan taron birnin Paris a kan 'yan gudun hijira, jaridar ta ce wasu kasashe hudu na kungiyar tarayyar Turai EU sun yi tayin ba da taimako ga kasashen Nijar da Libya da kuma Chadi da ke zama matattarar bakin haure da ke kwararowa zuwa Turai, matukar kasashen suka ba da ta su gudunmawa wajen dakile kwararar bakin haure. A gun taron kolin na Paris a ranar Litinin, wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakoncin shugabannin kasashen Spain, Jamus da Italiya, sai kuma na kasashen Nijar, Chadi da Libya, an tattauna kan yadda za a yanke hukunci ba da mafakar siyasa tun a Afirka. Kasashen Turan dai na son su fadada sansanin 'yan gudun hijira a kasashen na Afirka inda daga nan za a rika duba bukatunsu ko sun cancanci a ba su mafaka a Turai kafin a ba su izinin shiga Turai. A nasu bangaren shugabannin kasashen Afirka sun nemi karin kudin tafiyar da wannan aiki suna masu cewa tuni suka fara aikin hadin da kasashen na Turai. Sai dai za a dauki lokaci mai tsawo kafin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Jemen Schlepper lassen Migranten ertrinken
Hoto: picture-alliance/house 6 peter eisenmann
Südsudan Fußball Nationalmannschaft - Spieler Mamoutou Ndiye
Hoto: Getty Images/AFP/H. Kouyate

Wasan kwallon kafa don maganin tashe-tashen hankula inji jaridar Neues Deutschland a labarin da ta buga game da kasar Kenya tana mai cewa.

A kasar Kenya wasan kwallon kafa ya hada kan kabilu dabam-dabam magoya bayan jam'iyyun siyasa masu adawa da juna. A filin wasan kwallon kafa na unguwar Korogocho ba bu alamun wani tashin hankali, sabanin wanda aka gani bayan zaben ranar 8 ga watan Agusta da ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa. Kungiyoyin fafatuka suka bullo da dabarar shirya wasannin kwallon kafa tsakanin kabilu a wani mataki na samar da zaman lafiya da fahimtar juna abin da watakila 'yan siyasa suka kasa yi. Jaridar ta ce irin wannan matakin na shirya gasar kwallon kafa zai ba da gagarumar gudunmawar hana aukuwar tashin hankali da ake yawaita samu bayan zabe a Kenya. Dole ne kuma 'yan siyasa su yi koyi da kungiyoyin fafatukar.

A jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuwa, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci game da rikicin kasar tana mai cewa:

Senegal Senegalesische Soldaten
Hoto: Getty Images/Afp/Marco Longari

Bayan lafawa ta tsawon lokaci, fadace-fadace sun sake kunno kai a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda a makon da ya gabata kadai mutane 30 suka rasa rayukansu a rikici tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da ba sa ga maciji da juna. Duk da cewa ana danganta rikicin kasar da addini, amma a cewar jaridar gwagwarmayar neman rike riko da yankin nan mai arizikin karkashin kasa na arewa maso gabashin kasar na zama babban dalilin rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa a kasar. Kasancewa ikon gwamnati ya ta'allaka ne a Bangui babban birnin kasar, ba a kuma girke dakarun kasa da kasa a fadin kasar baki daya ba, zai wahala a shawo kan rikicin nan da lokaci kankani.