Slovenia ta amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa
May 30, 2024Slovenia ta sanar da bin sahun wasu kasashen Turai wajen amincewa da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta.
Firaministan kasar Robert Golob ne ya sanar da hakan a Alhamis din nan, yana mai cewar abin da ya rage shi ne mika batun gaban majalisar dokokin kasar watakil a mako mai kamawa, domin samun sahalewarta.
Karin bayani:Spain da Ireland da Norway sun amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa
Matakin na Slovenia ya biyo bayan irinsa da kasashen Spain da Ireland da kuma Norway suka dauka, har ma suka sanar a hukumance.
Karin bayani:Harin Isra'ila ya kashe jami'an agaji 7 'yan kasar waje a Gaza
Daga cikin kasashe 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya, sama da 140 daga cikinsu sun amince da bai wa Falasdinu 'yancin zama kasa, amma ba tare da samun hadin kan Amurka da wasu kasashen yamma ba.
A martanin da Isra'ila ta mayarwa Slovenia, ta yi fatan majalisar dokokin za ta yi watsi da wannan kuduri.