Soja za su daura damarar yaki a Somaliya
October 22, 2017Shugaban kasar Somaliya ya yi kira ga dakarun sojan kasar da su shirya damara ta yaki da mayakan al-Shabab wadanda ake zargi da hannu a harin bam da ya yi sanadi na rayukan mutane 350 baya ga raunata wasu 500 a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. A kwai dai har kawo yanzu gwammai wadanda suka bace bayan wannan mummunan hari da kasar ta gani a bayan nan.
Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed ya yi jawabin nasa ne gaban dakarun sojan kasar da dama a sansaninsu da ke kusa da babban birnin kasar a daidai lokacin da kuma wasu ke ci gaba da aiki na kwashe baraguzai na gine-gine da aka yi fata-fata da su a sakamakon harin, suna lalube na sauran jikkuna al'umma.
Mai magana da yawun sojan kasar dai ya ce za su yi aiki tukuru wajen ganin sun fatattaki mayakan na al-Shabab a wajen da suka fi karfi a kasar da ke a Gabashin Afirka. Ana sa ran dai Amirka za ta taka rawa a kokarin da dakarun za su sanya gaba wajen korar mayakan sakan.