1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan masar da ke son takara ya sha dauri

Mouhamadou Awal Balarabe
December 19, 2017

Wani hapsan sojin Masar Ahmed Konsowa ya sha daurin watanni shida a gidan yari bayan da ya bayyana aniyar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2018, lamarin da ya saba wa dokar sojoji.

https://p.dw.com/p/2pfhn
Screenshot Youtube- General Ahmed Konsowa
Hoto: Youtube

Wata kotun kasar Masar ta yanke wa wani kanal na soji hukuncin dauri watanni shida a gidan yari sakamakon bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa. Sai dai lawyan kanal Ahmed konsowa wanda ya bada wannan labarin ya ce za su daukaka kara.

Makonni biyun da suka gabata ne aka kama hapsan sojen na Masar bayan da a wani faifai na bidiyo a Youtube ya bayyana sauyin da zai kawo idan ya lashe zabe mai zuwa. Sai dai kuma doka ta haramta masa tsoma baki a harkokin siyasa a matsayinsa na wanda yake sanye da kakin soje.

Ana zargin shugaban kasar Masar Abdel Fatah a- Sisy da neman kawar da duk wadanda za su iya kawo tarnaki wajen hanashi zarcewa, ko da shi ke har yanzu bai bayyana aniyar tsayawa takara a zaben badi ba.