Sojojin Amirka za su bar Nijar a watan Satumbar 2024
May 19, 2024A cikin sanarwar hadin gwiwa da Amirka da kuma majalisar mulkin sojin Nijar suka fitar, sun ce sun cimma matsayar ne kan fara kwashe dakarun bisa bukatar gwamnatin sojin sakamakon zargin da ta yi na girke su ba bisa ka'ida ba.
Karin bayani: Amirka na shirin janye dakarunta daga Nijar
Kazalika bangarorin sun cimma yarjejeniyar bayar da kariya ga sojojin Amirka har zuwa lokacin da za a kammala janye su. Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da tawagar Amirka da sojojin Nijar suka kwashe kwanaki suna tattauna wa kan jadawalin aikin kwashe dakarun.
Karin bayani: Amirka na son ci gaba da yin hulda da Nijar
Tun bayan da sojoji suka kwace mulkin Nijar a shekarar 2023, majalisar sojin kasar ta soke yarjejeniyar tsaro tsakaninta da gwamnatin Washington tare da katse alakarta da uwargijiyarta Faransa, yayin da a gefe guda ta karfafa alaka da kasar Rasha.