1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SOJIN AMURKA 141 SUKA MUTU BAYAN YAKIN IRAQ:

JAMILU SANINovember 4, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnn

A kasar Iraqi yau aka bada labarin mutuwar sojin Amurka biyu,yayin kuma da yan asalin kasar ta Iraqi uku suka rigamu gidan gaskiya,irin wanan hali dai na nuni ne da cewa yan sari kanoken Iraqi na cigaba da kai hari kann sojin taron dangi na Amurka da Birtania dama fararen hula a kusan kowace rana ta Allah.
Wanan daili ne ma ya sanya Priministan kasar Spain Maria Aznar dake kawance da Amurka yace zasu dauki matakan rufe ofishin jakadancin kasar ta Spain dake birnin Bagadaza,kuma a janye dukanin jami'an dilomaciyar Spain daga cikin kasar Iraqi.
Mai magana da yawun sojin Amurka a kasar Iraqi,ya baiyana cewa tun da sanyin safiyar yau talata sojin Amurka biyu suka bakunci lahira,yayin da biyu kuma suka sami raunuka,bayan da wani abu mai kama da bomb ya fashe a birnin Bagadaza.
Kawo yanzu dai yawan asarar rayukan da ake cigaba da samu ta sojin Amurka a kasar Iraqi,ya kai 141 tun bayan da gwamnatin birnin Washington ta bada sanarwar kawo karshen yakin Iraqi ranar daya ga watan Mayun da ya gabata.
To saiu dai kuma in kwatanta yawan hare hare na kunar bakin waken da aka kaiwa sojin Amurka,za'a ga cewa lamarin sai abinda ya karu. Wanan adadi dai na yawan sojin Amurka 141 da suka rasa rayukan su a kasar Iraqi,ya hadar da sojin na Amurka na bataliya ta hudu da suka mutu jiya litini,tun bayan da wani bomb ya tashi a garin Tikirit mai tazarar kilomita 180 daga arewacin birnin Bagadaza.
A chan kuma garin Kirkuk na arewacin Iraqi,an bada labarin cewa sojin Amurka sun harbe wani mai sharia,a lokacin da yake kokarin kawai dakarun na Amurka hari na kwantan bauna,kamar yadda wanan sanarwar ta fito daga hukumomin yan sanda da kuma dan uwan wanan mai sharia na kasar ta Iraqi da aka ce shima ya sami raunka samakon harshashin da shiga jikinsa. A tsakiyar garin Karbala kuma na yan shiiter kasar Iraqi,an bada labarin mutuwar yan Iraqi biyu jiya litinin kusa da wani hotel dake bayan masalacin Al-Mukhayam.
Ganin yadda fararen hular Iraqi ke musayar wuta da sojin Amurka da sojin Amurka a kusan kowace rana ta Allah,ya sanya Pm kasar Spain ya bada sanarwar janye jami'an dilomciyar kasarsa dake Iraqi zuwa wani lokacin kamfin a sami ingantuwar harkokin tsaro a Iraqi.
Da yake jawabi ga manema labaru a birnin Berlin,bayan da ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Gehard Schroeder,PM kasar Spain Maria Aznar ya baiyana cewa sun dauki matakan janye jami'an dilomaciyar su daga kasar Iraqi ne,ba don komai ba sai don halin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Tun bayan harin bomb din ranar 19 ga watan Agustan da ya gabata hedkwatar majalisar dikin duniya dake birnin Bagadaza,ya sanya kungiyoyin bada agaji na kasahen duniya,suka fara kaura daga cikin kasar Iraqi.
Harin bomb din dai na ofishin majalisar dinkin duniya a kasar ta Iraqi,ya janwo mutuwar mutane 23,baya kuma ga harin bomb din da ya faru a hedkwatar kungiyar bada agajin kasa da kasa ta Red Cross a ranar 27 ga watan Octoban da ya gabata wanda kuma yayi sandiyar mutuwar mutane 43.
An dai baiyana cewa kasar ta Iraqi ta cigaba da fuskantar matsaloli na hare haren kunar bakin wake,wanda kuma aka zargi magoya bayan hambararen shugaban kasar Iraqi saddam Hussien da wanan laifi,koda yake hali na rashin tabas din zaman lafiya yafi kamari ne a garin Karbala.
Har kawo yanzu dai sojin Amurka na cigaba da binciko burbushin jirgen na mai saukar ungulu da aka kaiwa hari kwanaki biyu a garin Falluja,da yayi sandiyar mutuwar sojin Amurka 16,20 kuma suka sami ranuka.