SiyasaJamus
Burkina Faso: An kashe gwamman 'yan ta'adda
November 9, 2021Talla
Ma'aikatar tsaron kasar Burkina Faso ta ce wani sojanta daya ya rasu a yayin batakashin tare da kuma raunata wasu uku. Sai dai ko ba'idinsa rundunar tsaron ta Burkina Faso ta ce ta yi nasarar kwace muggan makamai a hannun mayakan ciki har da baburan da suke kai wa dakarun tsaron kasar hari da su.
Tun a shekarar 2015 ne dai kasar mai makwaftaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga masu tsananin kishin addini, inda rahotanni suka ce an halaka fiye da mutum dubu biyu, wasu fiye da miliyan daya suka kauracewa gidajensu don tsira da ransu.