1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin MDD sun fara janyewa daga Kwango

Abdullahi Tanko Bala
February 28, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta fara janye dakarunta na kiyaye zaman lafiya MONUSCO daga Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango inda ta mika ragamar sansanin ga rundunar yan sandan kasar ta Kwango.

https://p.dw.com/p/4czEA
Dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Hoto: MONUSCO/Xinhua/picture alliance

A yayin bikin da aka gudanar a hukumance a sansanin Kamanyola da ke kusa da iyakar Rwanda da Burundi, an maye gurbin tutar Majalisar Dinkin Duniya da Pakistan wadanda sojojinsu na kiyaye zaman lafiya ke kula da sansanin.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta bukaci janye dakarun kiyaye zaman lafiyar duk da damuwar da Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna kan yawaitar tashe tashen hankula a gabashin kasar Kwangon