1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Togo sun yi kuskuren kisan fararen hula

July 15, 2022

Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a yayin neman wasu 'yan ta'adda da suke yi a arewacin kasar, inda suka ba su ji dadin yadda bisa kuskure jirgin yakinsu ya halaka mutanen bakwai da dukkansu matasa ne ba.

https://p.dw.com/p/4EDe8
Soldaten aus Togo fliegen nach Mali
Hoto: picture-alliance/dpa

Rundunar sojin kasar Togo ta nuna kidimewarta a kan kisan da jami'anta da ke kan sintiri suka yi wa wasu fararen hula bisa kuskure. 
Neman afuwar da sojojin Togon suka yi, na zuwa ne a yayin da a yammacin Jumma'ar nan, rahotanni ke cewa mahara sun halaka wasu mutane 12 a wani hari da suka kai a arewacin kasar.