1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kame shugaban Mali

August 18, 2020

Sojojin kasar Mali, sun kame shugabannin kasar ne da yammacin wannan Talata bayan harbe-harbe. Wani na gaba-gaba cikin sojojin ne ya sanar da hakan.

https://p.dw.com/p/3h8nY
Mali Militärstützpunkt in Kati
Hoto: AFP/H. Kouyate

Dakarun masu bore a Mali, sun kame Shugaba Ibrahim Boubacar Keita tare da Firaminista Boubou Cisse, wani daga cikin na gaba-gaba cikin dakarun masu boren ne ya sanar da hakan.

Kamar dai yadda rahotanni ke tabbatarwa, an kame shugabannin na Mali a gidan Shugaban kasa da ke a Bamako babban birni.

Tun da fari dai sojojin na Mali sun tayar da kayar baya ne a sansaninsu da ke garin Kati, 'yar tazara birnin na Bamako.

Wasu majiyoyi na sojin da ba su so a bayyana su ba, sun ce an mike da Shugaba Keita da Firaministan Cissen ne cikin wata tankar yaki a kan hanyar zuwa garin Katin inda sansanin sojoji yake.

Da ranar wannan Talatar ce dai dakarun na Mali, suka fara wannan boren da aka fassara da yunkurin kifar da gwamnati.