Ana zargin juyin mulki a Burkina Faso
January 24, 2022Al'umma a burkina Faso na cikin rudani bayan da aka jiyo karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar Roch Marc Christain Kabore da ke Ouagadougou, yayin da wasu rahotanni ke ayyana hakan da zargin juyin mulki a kasar da ke fama da rikicin ta'addanci, ya zuwa wannan lokaci sojoji sun tabbatar da tsare shugaban kasa da shi da wasu ministocinsa. Wannan dai na zuwa ne bayan wani bore da sojojin suka yi na bukatar canza wasu shugabanninsu da ma neman karin kayayyakin yaki da mayakan jihadi da ke gwagwarmaya da makamai a kasar. A jiya Lahadi ne wani gungun matasa da ke bore a akan halin da kasar ke ciki suka cin nawa shelkwatar jam'iyyar Shugaba Kabore wuta. Ayyukan ta'addanci a kasar ta Burkina ya yi sanadin mutuwar rayukan mutane da dama tare ma da raba wasu da matsugunnansu.