1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikon kwarya na shekaru uku a Burkina Faso

Abdourahamane Hassane
March 1, 2022

Sabbin hukumomin mulkin soji a Burkina Faso sun kayade wa'adin mulki na gwamnatin rikon kwarya har tsawon shekaru uku kafin gudanar da sabbin zabubka domin sake mayar da kasar bisa tafarki na demokaradiyya.

https://p.dw.com/p/47l9b
Burkina Faso | Militärleiter Paul-Henri Sandaogo Damiba
Hoto: Radiodiffusion TÈlÈvision du Burkina/AFP

An dai ba da wannan sanarwa ce a karshen wani taro na kasa da aka gudanar wanda ya hada sojoji da wakilai na kungiyoyin fara hula da sauran masu fada a ji na kasar. A cikin shirin dokar da aka cimma a taron wadda shugaban ya sa hannu a kai, ta tanadi cewar shugaban gwamnatin rikon kwarya Paul Henri Sandaogo ba zai tsaya takara ba a zaben shugaban kasa,ko na 'yan majalisa dokoki ko kuma na kansila a karshen wa#adin aikin gwamnatin wucin gadin.