Sojojin ƙasar Aljeriya sun kai hari akan 'yan Aqmi
December 11, 2010Dakarun gwamnati a ƙasar Aljeriya sun kashe masu fafutukar kishin Islama guda goma a sa'ilin wani samamen da suka kai a gabacin Kabylie inda nan ne cibiyar 'yan ƙungiyar Al-Kaida reshen Aqmi. Sojoji kamar dubu huɗu da kuma jirage masu saukar ungulu dake rufa masu baya suka yi ɓarin wuta a yankin Tizi Ouzou. Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya shaida cewa sojojin sun kai farmakin ne saboda labarin da suka samu daga hukumar leƙen asiri ta ƙasar, cewa akwai wata haɗuwa ta gudanar da wani taron na 'yan ƙungiyar ta Al-Kaida a yankin.
Ƙungiyar ta Aqmi tana tsare da wasu 'yan ƙasar Faransa guda biyar da take yin garkuwa da su wanda ta sace watanni ukku da suka wuce a arewacin ƙasar Nijar.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal