1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan na fuskantar barazanar tsaro

Abdourahamane Hassane
July 6, 2021

Dubban sojoji na Afghanistan sun arce daga fagen yaki suka shiga Tajikistan da ke kan iyaka da kasar bayan wani mummumar gumurzu da  dakarun Taliban a arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3w51e
Afghanistan Regierungstruppen in Faizabad
Hoto: Afghanistan Ministry of Defence/REUTERS

'Yan taliban din sun karpe goman garurruan da ke a karkashin ikon gwamnatin abin da ya sa ake da fargaban faduwar gwamnatin ta Afghanistan. Yanzu haka Tajikistan ta tura sojoji sama da dubu 20 a kan iyakarta da Afghanistan yayin da Rasha ta rufe ofishin jakadancin  a birnin Kabul. Masu aiko da rahotanin sun ce ficewar sojojin kawance na kasashen duniya daga Afghanistan ya kara dagula al'amuran tsaro a kasar.