1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi: Rakiya ga sojojin Faransa

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 14, 2023

Chadi ta sanar da cewa sojojinta za su raka na uwar giyarta Faransa kimanin 1,400 da za su bi ta kasarata, biyo bayan korar da gwamnatin juyin mulkin sojan makwabciyar kasa Jamhuriyar Nijar ta yi musu.

https://p.dw.com/p/4XXfG
Nijar | Yamai | Sojoji | Faransa | Rakiya | Chadi
Nijar ce kasa ta biyu a yankin Sahel bayan Mali da aka kori sojojin FaransaHoto: picture-alliance/AP Photo/French Defense Ministry/M. Buis

A yanzu dai sojojin Faransan na fita da kayan aikinsu mafi yawa ta kasa ne tare da bi ta Chadi da Kamaru, hanyar da ke da nisan sama da kilomita 3,000 da kuma ke da tarin 'yan ta'adda. Cikin wata sanarwa ne dai, babban hafsan hafsoshin Chadin Abakar Abdelkerim Daoud ne ya bayyana hakan, inda ya ce sun amince ta samar da hanyar da korarrun sojojin uwargijiyar tasuFaransa daga kan iyakar Nijar zuwa N'Djamena domin isa filin jirgin sama zuwa tashar jiragen ruwa ta Douala a Kamaru kaana su dangana da kasarsu.