1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin ECOWAS za su kitsa dabaru kan Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
August 15, 2023

Bayan dage taron farko da suka shirya gudanarwa, hafsoshin sojojin kasashen yammacin Afirka za su yi zama a Accra cikin kwanaki biyu masu zuwa don shirya dabarun tinkarar sojojin Nijar.

https://p.dw.com/p/4VCGh
Manyan sojojin Guines Bissau na daga cikin wadanda ECOWAS za ta tura NijarHoto: Präsidentschaft der Republik Guinea-Bissau

Shugabannin rundunonin sojojin kasashen yammacin Afirka sun shirya gudanar da taro a birnin Accra na Ghana daga ranar Alhamis, da nufin tattauna yiwuwar kutsawa da makamai Nijar domin mayar da shugaba Mohamed Bazoum a kan kujerar mulki. Wannan taron da aka fara dage shi, ya zo ne lokacin da shugaban  Rasha Vladimir Putin da shugaban mulkkin sojan Mali Assimi Goïta suka jaddada mahimmancin warware rikicin na Nijar ta hanyar diflomasiyya.

A baya dai, Kasar Mali mai makwabtaka da Nijar ta nuna goyon bayanta ga sojojin da suka yi juyin mulki tare da nuna barazanar da ke tattare da afka wa Nijar da makamai. Sai dai a nata bangaren, kungiyar ECOWAS/CEDEAO ta yi Allah wadai da abin da ta danganta da "tsokana" da sojojin da ke rike da madafun iko a birnin Yamai suka yi, bayan da suka bayyana aniyarsu ta gurfanar da hambararren Shugaba Bazoum a gaban kuliya bisa laifin cin amanar kasa.

Shugabannin addinai da shugabannin siyasa da dama a arewacin Najeriya na kara kaimi wajen cimma matsaya ta diflomasiyya don magance rikicin shugabancin Nijar da kuma kauce wa amfani da karfi.