Sojojin Guinea sun rusa jam'iyyu da dama a kasar
October 29, 2024Baya ga rusa jam'iyyun, gwamnatin ta kuma kafa kwamitin da zai sanya ido kan ayyukan wasu jam'iyyu kimanin 67 a cikin watanni uku domin tabbatar da cewa sun tsallake siradin tantancewa da kuma tabbatar da doka da oda a fadin kasar, duk da cewa hukumomin sojin ba su sanar da ranar da za a gudanar zabe ba.
Karin bayani: Guinea Conakry za ta yi zaben kasa a 2025
Tun a shekara ta 2021 sojojin kasar ta Guinea suka hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde da Kungiyar ta ECOWAS ke kiraye-kirayen dawo da mulki kan tafarkin dimukradiyya a kasar zuwa shekara ta 2025.
Karin bayani: Guinea Conakry: Shakku kan alkawarin zabe
Kasar Guinea Conakry na daya daga cikin kasashen da suka hambarar da gwamnatocin farar hula a yammacin Afirka da suka hada da Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso wacce a baya-bayan nan sojojin da ke kan karagar mulki suka sanar da cewa sai nan da shekaru biyar zasu gudanar da zabe a kasar.