Sabon taron ECOWAS kan Nijar
August 9, 2023Majalisar ta CNSP karkashin janar Abdourahamane Tiani ta yi tsayuwar gwamen jaki kan duk kiraye-kirayen da kungiyar raya tattalin kasashen Yammacin Afrika da kuma wasu kasashen Yamma suka yi mata domin mayar da hambararren shugaban kasa kan kujerarsa.
A cikin wannan yanayi na mai abu ya rantse marar abu ya rantse ne shugabannin kasashen ECOWAS da tun farko suka kakaba wa Nijar takunkumai za su tattauna a Abuja domin fito da sabuwar dabara.
Sai dai a jajibirin taron shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ke jagorantar kungiyar ya kawar da maganar daukar matakin soja kan Nijar wanda tun farko aka sanar inda ya ce za a fifita hanyoyin diflomasiyya don warware lamarin cikin ruwan sanhi kamar yadda wasu manyan kasashe ciki har da Jamus da Italiya da Amurka suka bukata.
A jajibirin taron ma dai sojojin na Nijar sun ki karbar wata tawaga da ECOWAS ta aike domin tattaunawa sabili da dalilai na tsaro da kuma dakauce mata fadawa cikin fushin al'umma sakamakon takunkumai masu tsauri da kungiyar ta kakabawa kasar tun farkon juyin mulki.