1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Nijar sun halaka 'yan ta'adda

Gazali Abdou Tasawa ZMA
November 17, 2023

Rundunar sojin kasar Nijar ta sanar da halaka wasu 'yan ta’adda kusan 10 wadanda suka kai hari a wata makarantar boko a cikin karamar hukumar Sanam ta jihar Tillabery.

https://p.dw.com/p/4Z2xs
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan tasirin da ake sa ran kwato birnin Kidal da sojojin Mali suka yi da kuma hada kan da sojojin kasashen Nijar da Mali da Burkina suka yi tun bayan ficewar sojojin Faransa, za su yi a fannin yaki da ta'addanci a yankin Sahel baki daya.

A ranar Alhamishin jiya ne dai ‘yan ta'addan asaman babura suka kai hari a makarantar ta kauyen Maichilmi ta karamar hukumar Sanam cikin Jihar tillabery, inda suka kona makarantar tare da ma da kaddamar da wa'azi a gaban dalibai da malaman makarantar.

To sai dai awoyi kalilan bayan haka, a daidai lokacin da 'yan ta'addan ke ganin tamkar sun ci gari,sojojin gwamnatin Nijar da ke sintiri a yankin suka kaddamar da farmaki kansu, inda suka yi nasarar fatattakarsu tare da halaka takwas daga cikinsu da kuma karbe tarin babura da bindigogi.

Gawarwakin 'yan ta'addan yashe a gaban mutanen kauyen, na yanzu ci gaba da yawo a saman shafukan sada zumunta a kasar ta Nijar. Tuni dai wasu 'yan kasar ta Nijar suka soma bayyana gamsuwarsu da wannan nasara da sojojin kasar ta Nijar suka samu kann 'yan ta'addan.

To amma Malam Sadik Abba wani mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Sahel, cewa ya yi nasarar da sojojin Nijar din ke samu ba abin mamaki ba ne a bisa wasu sauye-sauye da aka samu a yankin.

To sai dai daga nashi bangare Malam Soule Oumarou na kungiyar FCR ya ce bai kamata ba wannan nasara ta sa a manta da kamarin da ta‘addanci ke yi a wasu yankunan kasar da kuma mahukunta ba sa yin bayani kansu.

Ko a makonni da suka gabata dai ‘yan ta'adda sun kaddamar da farmaki a wata makaranta kusa da garin Makalondi inda suka yi awon gaba da malamai biyu wadanda har yanzu babu duriyarsu. Yanzu haka wasu alkalumman  gwamnatin kasar sun nunar da cewa akawai makarantu firamare da na sakandare 921 da matsalar tsaro ta tilasta rufe su a a jihar Tillabery.