1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojin sun nemi agajin Wagner

August 6, 2023

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ce jagoran juyin mulki Janar Salifou Mody ne ya gabatar da bukatar ga sojojin Rashan a yayin wata ziyara da ya kai Mali.

https://p.dw.com/p/4UoyA
Jagoran gwamnatin mulkin soji ta Nijar Janar Tchiani
Jagoran gwamnatin mulkin soji ta Nijar Janar Tchiani Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Sojojin Nijar sun nemi dauki daga sojojin kamfanin tsaron Wagner mallakin kasar Rasha daidai lokacin da wa'adin da shugabannin kasashen yammacin Afirka suka ba su na su dawo da hambararren shugaba kan kujerarsa ke cika a wannan Lahadi.

A yayin da yake kammala ziyarar da ya kai kasar Mali wacce sojoji masu juyin mulki ke jagoranta a ranar Juma'a, Janar Mody na Nijar, ya yi gargadi a kan yunkurin da ake yi na turo sojin kasashen ECOWAS su yake su, yana mai cewa Nijar za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare kanta daga zama wata sabuwar kasar Libya.

Sojojin dai na da sa'o'i kalilan kafin wa'adin kwanaki bakwai da aka diba musu na su saki Shugaba Bazoum wanda ya ce suke garkuwa da shi sannan kuma su mayar da shi kan mukaminsa. Idan har suka gaza yin hakan, kasashe mambobin ECOWAS na iya amfani da karfi wajen tunkarar sojin Nijar din.