Sojojin Somaliya sun murkushe 'yan bindiga
July 13, 2019Jami'an tsaron Somaliya sun bayyana cewa sun yi nasarar murkushe 'yan bindigan Al Shabaab da suka kai hari a cikin dare a wani otel na birnin Kismayu da ke kudancin kasar. Wani babban jami'in 'yan sanda Major Mohammed Abdi ya bayyana wa manaima labarai cewar akalla 13 sun rasa rayukansu yayin musayar wuta tsakanin bangarorin biyu ciki har da 'yan bindiga hudu da suka kai harin. Ya kuma kara da cewa an yi nasarar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su.
Su dai 'yan bindigan da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda sun mamaye otel din ne bayan da suka girke mota shake da bama-bamai a jiya Jumma'a yayin da dattawan yankin Kismayu da kuma 'yan majalisa suka taru don tattaunawa game da zaben yankin da ke karatowa. Ita dai Somaliya ta saba fuskantar hare-hare daga 'yan al Shabaab duk da nasarar fatattakarsu da aka yi daga Mogadishu.