1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin sojojin Wagner a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
February 28, 2023

Sojojin haya na Wagner da ke da kusanci da gwamnatin Rasha sun rubanya ayyukan da suke gudanarwa a wasu kasashen Afirka a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4O4x5
Mali Wagner-Söldner
Hoto: French Army/AP/picture alliance

Sojojin haya na Wagner da ke da kusanci da gwamnatin Rasha sun rubanya ayyukan da suke gudanarwa a wasu kasashen Afirka. Amma dai a lokacin da suka bayyana a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun kasance a matsayin wadanda suke nuna rashin sani don magance matsalar tsaro da ake fama da ita.

Da farko, aikin sojojin Rasha a Afirka ya fara zama jita-jita kafin ya karade kanun labaru, inda dubban sojojin na haya suka yadu zuwa kasashen wannan nahiya da dama. A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ga misali,  jakadan Rasha a kasar ya ce, masu horar na kasarsa sun tallafa wa dakarun gwamnati a yakin basasa da ta fuskanta. Sannan kimanin sojojin hayar Wagner 1,200 suna tallafa wa madugun 'yan tawaye Libiya Chalifa Haftar a fafatawa da yake don kankange madafun iko. Hakazalika masu lura da al'amuran yau da kullum suka ce, gwamnatin mulkin sojojin Mali ta shigar da daruruwan mayakan Wagner cikin kasar, wadanda ake zargi da take hakkin bil'adama. Amma masana harkokin tsaro suna jan hankali kan wuce gona da kungiyar Wagner ke yi a kasashen Afirka.

Kasar Rasha na neman kara yin tasiri a nahiyar Afirka, saboda haka ne Kungiyar Wagner ta zame mata damba baya ga ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov ke gudanarwa. Sannan fadar mulkin ta Moscow na rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tsaro da hada-hadar makamai da kuma a wasu lokuta, isamar da abinci da taki kyauta ga wasu kasashen Afirka. Amma kuma a matsayin godiya, Rasha ta samun goyon bayan kasashe 15 na Afirka da suka zama 'yan ba ruwanmu a kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan yakin Ukraine, a yayin da Iritiriya da Mali suka goyi bayan Rasha kai tsaye.

Bincike na kasa da kasa ya bayyana cewa Kungiyar Wagner na aiki a wasu fannoni da ba su da dangantaka ta tsaro, ko da watan Yulin da ya gabata, sai da wasu kafofin watsa labarai 11 na Turai, suka bayyana cewa gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ba wa Wagner hakkin hakar ma'adinai a kadada 187,000.

A tsibirin Madagaskar ma, hukumomi sun janye takardun wani kamfanin hakar ma'adinai na Kanada domin danka wa wagner. Binciken da Mujallar The Africa Report ta yi ya nuna yadda cibiyar sadarwa ta Wagner ta ce, ta shigo da manyan na’urorin hakar ma’adanai ta tashar ruwan Douala ta Kamaru.

Yanzu haka ana shirya ayarin motocin dakon kaya har uku daga Bangui zuwa Douala a duk mako domin jigilar kayan bisa kariyar sojojin haya na Kungiyar Wagner. Wannan na iya zama wata dama ga gwamnatocin Afirka da ke fuskantar matsalar karancin kudi na saka wa kungiyar da wasu kangiloli hakar ma#adinai.