Holland da Birtaniya sun soma zaben EU
May 23, 2019Talla
Mutane kimanin miliyan 400 masu rijistan zabe a kasashen 28 na Turai za su zabi 'yan majalisar dokokin Turai guda 751. An dai bude runfunan zaben ne tun da misalin karfe biyar da rabi agogon JMT a kasar ta Hollande mai kujeru 26 a majalisar Turan.
Alamu na nuni da cewa jam'iyyar FVD mai akidar adawa da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma kyamar 'yan gudun hijira ta Thierry Baudet dan shekaru 36 ce za ta zo a matsayi na daya a zaben.
A Birtaniya kuma mai shirye-shiryen ficewa daga Kungiyar ta EU da kuma ke da kujeru 73 a cikin majalisar Turan an bude runfunan zaben ne a karfe shida agogon GMT.