Hare-haren 'yan tawaye a Somaliland
February 17, 2023Mai magana da yawun Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar UNCHR Olga Sarrado Mur ce ta sanar da hakan a birnin Geneva na kasar Swetherland, inda ta ce mafi yawan wadanda suka tsere din mata ne da kananan yara. Ta kara da cewa 'yan gudun hijirar sun fito ne daga birnin Lasanod da ke arewacin kasar, kuma suna kwana a cikin azuzuwan makarantu da gine-ginen da ba su da rufi. A cewarta mutanen na bukatar tallafin jin-kai cikin gaggawa, musamman ma na abinci da ruwan sha da kuma wurin zama mai tsabta. Rahotanni sun nunar da cewa, 'yan tawayen birnin na Lasanod na fafatawa da sojojin yankin Somaliland da ya ayyana cin gashin kansa. Tun dai a shekara ta 1991 yankin na Somaliland ya ayyana ballewa daga Somaliya, sai dai hara kawo yanzu bai samu amincewar al'ummomin kasa da kasa ba.