Somaliya: Jami'an tsaro sun kashe mutane
April 13, 2019Baya ga direban da aka kashe, jami'an tsaron sun kuma sun harbe fasinja da ya ke dauke da shi. Wannan batu dai ya sanya mutane da dama a birnin musamman dai samari fantsama kan titutna don nuna rashin amincewarsu da kisan, inda nan kuma jami'an tsaron suka harbe masu zanga-zanga hudu.
Masu aiko da rahotanni suka ce 'yan sanda sun harbe masu zanga-zangar bayan da suka rika jifansu da dawatsu da kuma kona tayoyi a manyan titunan birnin kafin daga bisani su yi yunkurin shiga fadar shugaban kasar ko da dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Magajin garin birnin na Mogadishu Abdulrahman Omar Osman wanda ya yi Allah wadai da kisan da aka yi, ya bukaci al'ummar birnin da su kwantar da hankalin kuma a cewarsa tuni 'yan sanda sun shiga farataur jami'an tsaron da ya yi kisan don ganin ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata.