1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Mutane sun rasa rayukansu a harin Mogadishu

Abdourahamane Hassane
May 22, 2019

Majiyoyin kiwon lafiya a Somaliya sun ce akalla mutane guda biyu suka mutu kana wasu 12 suka jikata a sakamakon harin da wani dan kunar bakin wake ya kai da mota makare da bama-bamai a  birnin Mogadishu.

https://p.dw.com/p/3Itcy
Somalia Anschlag in Mogadischu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Abdi Warsameh

Harin wanda aka kai a kusa da wani wurin tsayawar motoci a Daljirka da ke a wajen Mogadishu ya hada da fararan hula da kuma jami'an tsaro. Ko da shi ke ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin amma dai ana kyautata zaton cewar kungiyar Al- Shebaab ita ce ke da alhaki.