1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MMD: Ana fama da matsalar yunwa a Somaliya

Abdullahi Tanko Bala
June 5, 2019

Mutane da dama a Somaliya na cikin hadarin mutuwa a sakamakon fari da ya haddasa kanfar abinci da ruwan sha yayin da a waje guda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran taimakon jinkai.

https://p.dw.com/p/3JvDy
Schweiz Genf UN Hauptquartier Mark Lowcock
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Keystone/S. Di Nolfi

Babban jami'in bada agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Marl Lowcock yace mutane fiye da miliyan biyu a Somalia maza da mata da kananan yara za su fuskanci matsananciyar yunwa a sakamakon fari idan ba a gaggauta kai wa kasar dauki ba.


Mark Lowcock yace ana bukatar kimanin dala miliyan 700 domin tallafawa jama'ar bayan da karancin ruwa ya lalata amfanin gona da kuma kashe dabbobi masu yawa.


Yace a halin da ake ciki hukumar ta karbi dala miliyan 45 domin cike gibin abinci da ruwan sha a kullum ga jama'ar da farin ya shafa a Somaliya da kuma Habasha