1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da mummunan hari a Somaliya

Yusuf Bala Nayaya
October 14, 2018

Somaliya ta yi tuni da shekara guda na mummunan hari da ba ta taba ganin irinsa ba, inda babbar mota makare da bama-bamai ta kai hari tsakiyar birnin Mogadishu inda ta halaka sama da mutane 500.

https://p.dw.com/p/36WI0
Somalia Mehr als 260 Tote nach Doppel-Anschlag in Mogadischu
Hoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

Yayin da mutane suka hadu a wurin tuni da mutanen da suka rasu inda suka tsaya tsit na minti guda, mutumin da ake zargi da kitsa kai harin an aika shi lahari ta sanadin aikin jami'an tsaro kamar yadda Capt. Mumin Hussein mataimakin mai gabatar da kara a babbar kotun Somaliya ya tabbatar da kisan na Hassan Aden Isaq, karon farko karkashin gwamnatin Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed.

Hare-hare dai sun yawaita a kasar ta Somaliya inda kungiyar al-Qaida da ke da alaka da al-Shabab ke ikirari na hannunsu akai irin wadanna hare-hare. Sai dai muni da harin na ranar 14 ga watan Oktobar bara da ya yi al-Shabab ba ta yi ikirari na cewa itra ke da hannu wajen kai shi ba.