Hukunci dauri kan shugabannin Kataloniya
October 14, 2019Kotun kolin kasar Spain ta yanke hukuncin dauri na shekaru tara zuwa 13 ga tara daga cikin jagororin 'yan awaren yankin Kataloniya su 12 da aka gurfanar a gabanta a bisa rawar da suka taka wajen neman ballewar yankin a shekara ta 2017. Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan da ta samu mutanen da laifin cin amanar kasa da kuma almundahana. Kotun ta ci sauran mutanen uku ministoci a tsohuwar gwamnatin ta yankin Kataloniya tarar kudi Euro dubu 60 da kuma haramcin tsayawa duk wata takara a watannin 20 masu zuwa
Sai dai kuma tuni tsohon shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont wanda ke zaman gudun hijira a kasar Beljiyam tun a shekara ta 2017 ya yi tir da Allah wadai da wannan hukunci tare ma da yin kira ga al'ummar yankin na Kataloniya kan lokaci ya yi da ya kamata ta tashi ta kara azama a gwagwarmayar kwatar 'yancin al'ummar yankin da kuma Demukuradiyya. Yanzu haka dai kotun kolin kasar ta Spain ta sake bayar a wannan Litinin da wani sabon sammacin kasa da kasa na neman kamo Carles Puigdemont.