Spain: Kotu ta tsare wasu jagororin aware
October 17, 2017Talla
Wata kotu a Spain ta bada umarnin tsare wasu manyan jagorori biyu na kungiyoyin 'yan awaren Kataloniya kan zargin tunzura jama'a su bijirewa gwamnati. Alkalin kotun yace mutanen biyu Jordi Sanchez da Jordi Cuixart sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen cusawa jama'a akidar bijirewa hukumomi a fafutukar neman ballewa domin samun 'yancin kan kasar Kataloniya.
Sai dai a wani mataki na nuna goyon baya ga mutanen da aka kama kimanin mutane 200 suka yi dandazo a fadar gwamnatin a Barcelona domin baiyana bacin ransu.
Wani mai goyon bayan ballewar yankin na Kataloniya Luis Gil yace matakin kotun abin mamaki ne domin mutanen su na gwagwarmayar neman 'yanci ne cikin lumana da kwanciyar hankali.