1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain na neman sulhu da Kataloniya

Lateefa Mustapha Ja'afar'October 5, 2014

Firaministan ƙasar Spain Mariano Rajoy ya yi kira da a kwantar da hankula tare kuma da buƙatar tattaunawa da 'yan yankin Kataloniya.

https://p.dw.com/p/1DPzu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Fernandez

Wannan mataki na Firaministan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da suke ci gaba da dagewa a kan bakansu na kaɗa ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a dangane da ci gaba da kasancewarsu a Spain ɗin ko kuma su ɓalle. Shugaban yankin na Kataloniya Artur Mas ya ce za su kaɗa ƙuri'ar ɓallewa daga Spain duk kuwa da ƙoƙarin hanasu da kotun tsarin mulkin ƙasar ke yi. Al'ummar yankin na Kataloniya sama da miliyan bakwai dai sun jima suna ƙorafin rashin adalci daga mahukuntan Madrid inda suke neman 'yancin cin gashin kansu. Yankin Kataloniya da ke da kimanin kaso 16 cikin 100 na al'ummar Spain, shi ne yankin da ya fi ko wanne arziki a ƙasar.