Spain: Ko masu ra'ayin rikau za su yi mulki?
July 24, 2023Tambaya ita ce shin Firaminista Pedro Sanchez mai ra'ayin gurguzu zai iya sake dawowa kan madafun ikon kasar ta Spain bayan zabe? Babu bangaren da ya samun rinjaye tsakanin bangaren masu matsakaicin ra'ayin mazan jiya da kuma masu ra'ayin gaba-dai gaba-dai. Tun shekara ta 2018 Firaminista Pedro Sanchez yake rike da madafun ikon kasar ta Spain kuma akwai yuwuwar ya tsallake yunkurin masu ra'ayin mazan jiya na kwace madafun iko daga hannunsa, amma yana da sauran kalubale mai yuwuwa na hada kai da 'yan Kataloniya da a baya suka yi yunkurin ballewa daga kasar. Josep Lluís Mestres dattijo masanin harkokin sinima wanda ya kada kuri'a a zaben na Spain yana da fata kan kafa gwamnatin hadaka : "Abin da yake da muhimmancin shi ne shi tsayar da masu matsanancin ra'ayin mazan jiya. Shi ne abin da ake tsoro sakamakon kuri'ar jan ra'ayi da aka gani kowace rana."
Alberto Nunez Feijoo na jam'iyyar Popular Party (PP) ya samu koma baya a zaben
Sakamakon zabe ya zama gagarumin koma-baya ga Alberto Nunez Feijoo na jam'iyyar Popular Party (PP) mai matsanancin ra'ayin mazan jiya da ya yi yunkurin kwace madafun ikon kasra kai tsaye lokacin zaben na karshen mako, amma kuma ya rasa samun yawan kuri'un da yake bukata wajen kafa gwamnati, inda ya samu kujerun majalisa 169 maimakon 176 da ake bukata wajen kafa gwamnati a majalisar dokokin mai kujeru 350. Ita kuma jam'iyyar gurguzu ta Firamnista Sanchez ta samu 153. Ga mutane irin Marisa Rodrigues masaniya kan tsirai tana goyon bayan kafa gwamnatin hadaka maimakon sabon zabe: "Na yi zabi domin kauce wa samun masu matsanancin ra'ayin mazan jiya kamar abin da ake gani a wasu kasashen Turai. Babu bukatar sake zuwa sabon zabe. Ina gani ya dace su cimma matsaya kan samun sabuwar gwamnati maimakon wani zabe."
Firaministan Spain na son girka kawance da 'yan yankin Kataloniya
Masu kada kuri'a da dama a Barcelona suna bukatar ganin firamnitsan ya hada kai da 'yan yankin wajen kafa gwamnati. Ga Sergi Pons mai zane-zaben gidaje jigo a jam'iyyar 'yan Kataloniya, yana ganin har yanzu jam'iyyar gurguzu da take rike da madafun iko karkashin Firaminista Pedro Sanchez take da dama kuma yana gani ya dace jam'iyyar ta ci gaba da jan ragamar kasar muddun ga misali suka hada gwiwa da bangaren 'yan Kataloniya: "Akalla bangaren Pedro Sanchez suna da sauran damar kafa gwamnati idan ya yi wani abu ga bangaren mu. Idan ba haka ba akwai yuwuwar sake komawa zabe. Saboda haka idan gwamnatin ta ba mu wani abu ba batun samun 'yancin kan Kataloniya ba, amma wani abi a bangaren tattalin arziki." Kasashen da dama musamman na Turai sun zuba ido domin ganin yadda za a kaya a zaben na Spain.