Spain ta baukaci taimako don tinkarar kwararar bakin haure
May 20, 2006Talla
Gwamnatin kasar Spain ta bukaci KTT EU da ta kara taimaka mata wajen tinkarar matsalar kwararar ´yan Afirka da ke kokarin shiga tsibiran Canaries. Gwamnati a birnin Madrid ta ce ta fara wani shiri na shekaru 3 ta fuskar diplomasiya a Yammacin Afirka da nufin dakile kwararar bakin haure daga Afirka zuwa nahiyar Turai. A kowace shekara dubban bakin haure kan bi ta hanyoyin masu hadari na teku a kokarin shiga cikin tsibiran Canaries da ma Spain din kanta. To amma da yawa daga cikin ´yan Afirka kan rasa rayukansu a cikin teku a kokarin su na shiga yankin na Spain, wanda suke gani a matsayi matakin farko na shiga nahiyar Turai. Daukacin bakin hauren dai ´yan tsakiyar Afirka ne da kuma kasashen Afirka kudu da Sahara.