1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain ta ceto 'yan Afirka daga Teku

Abdul-raheem Hassan
July 28, 2018

Masu ayyukan ceto sun ce cikin kwanaki biyu sun ceto sama da bakin haure 1,000 daga nutsewa a Tekun Baharmaliya, kuma sun ce mutanen sun fito ne daga arewacin Afirka sun nufi Turai.

https://p.dw.com/p/32FXV
Spanien Hunderte Flüchtlinge stürmen in spanische Nordafrika-Enklave
Hoto: imago/Agencia EFE/Reduan

Da frako masu ayyukan ceton sun fara fitar da mutane 774 da ke cikin jiragen ruwa daban-daban har 52, kamin daga bisani jami'an agajin sun yi nasarar fitar da wasu mutane 206 daga jirage 10 da ke yunkurin kifewa a cikin Teku.

A yanzu dai kasashen Aljeriya da Moroko ne ke zama kofar da bakin hauren Afirka ke bi tun bayan da Libiya ta killace iyakokinta da kasar Italiya. An kiyasta cewa akalla bakin haure dubu 20 sun shiga Spain ta ruwa a shekarar 2018.