Spain ta dakatar da 'yancin Kataloniya
October 28, 2017'Yan sa'o'i bayan ayyana samun 'yancin kai da majalisar dokokin Kataloniya ta yi, firaministan kasar Spain ya dauki wasu tsauraran matakan dakatar da tabbatuwar hakan, inda ya sanar da rusa shugabanni da ma majalisar dokokin yankin. Dama dai 'yan majalisa 70 cikin 80 ne dai suka amince da ballewar yankin daga ikon gwamnatin Spain din.
Tuni dai Faraministan na Spain, ya yanke shawarin cewa za a gudanar da zabe a Kataloniyan ranar 21 ga watan Disambar bana, saboda abin da ya kira kokari na dawo da daidaito a yankin. Tun da fari dai sai da kotun tsarin mulki a Spain ta yanke hukuncin cewa matsayin da majalisar Kataloniyar ta dauka na ballewa, ya saba wa doka. Dambarwar gwamnatin da yankin na Kataloniya dai wata aba ce da ke kokarin zama ala-kakai a siyasar nahiyar Turai.