1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karo na biyu Spain ta lashe irin wannan gasa

Mouhamadou Awal Balarabe AAI
September 16, 2019

Nasarar da Spain ta samu na zama zakara a gasar duniya ta kwallon kwando ya sa 'yan wasan kwallon kwandon Najeriya da ke sha'awar wasan sun fara fadi tashin ganin lallai suma ba a barsu a baya ba

https://p.dw.com/p/3Pgnm
Kungiyar kwallon kwando ta kasar Spain yayin da suke fafatawa a gasar
Kungiyar kwallon kwando ta kasar Spain yayin da suke fafatawa a gasarHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schiefelbein

A cikin shirin za a ji yadda a fannin kwallon kwando, kasar Spain ta yi nasarar zama zakarar duniya na Basketball bayan da ta doke Argentina da ci 95 da 75 a wasan karshe da ya gudana a kasar Chaina! Wannan dai shi ne karo na biyu da Spain ta zama gawani na gwanayen duniya a wasan kwallon kwando cikin 13 da suka gabata. 'Yan wasanta biyu ne kawai suka dama a babbar kungiyar kwallon kwando na Spain lokacin da ta zama ta daya a duniya ciki har da Marc Gasol wanda karkashin kungiyar Toronta ya lashe kofin NBA a watan Yunin da ya gabata. Kasar Faransa ce ta samu matsayi na uku sakamakon samun nasarar da ta yi a kan Austreliya da ci 67 da 59 a wasan neman matsayi. 

A fagen kwallon kafa kuwa, lissafin Bayern Munich ya dagule a teburin Bundesliga bayan da ta yi karon bata da Lepzig da ke ci gaba da jan zarenta ba tare da ya tsinke ba. za a ji sauran labaran wasannin a cikin shirin.