1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain za ta sake ɗaukar matakan tsumi

September 27, 2012

Gwamnatin Spain ta ce za ta tsuke bakin aljihu a wani mataki na tabbatarwa da takwarorinta na ƙasashen Turai yunƙurin da ta ke na cike giɓin kasafin kuɗin ta.

https://p.dw.com/p/16Gg5
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Spanish Prime Minister Mariano Rajoy poses after arriving for an interview on national Spanish Public Television (TVE) in Madrid September 10, 2012. REUTERS/Susana Vera (SPAIN - Tags: POLITICS)
Spanien Premierminister Rajoy TV InterviewHoto: Reuters

Shirin na ƙunshe ne cikin kasafin kuɗin baɗi da gwamnatin ta gabatar inda ta bayyana cewar za ta rage irin kuɗaɗen da ake ɓatarwa a gwamnatance domin Spain ɗin ta kai ga cimma wannan buri na ta.

Da ya ke jawabi game da wannan matakin, ministan kuɗin ƙasar Cristobal Montoro ya ce a cikin kasafin kuɗin na baɗi gwamnati za ta tsuke bakin aljihunta wanda zai bata damar yin tsumin dala biliyan hamsin da ɗaya.

A nata jawabin game da matsayin da gwamnatin ta ɗauka, muƙaddashin firaministan ƙasar Soraya Saenz de Santamaria ta ce kasafin kuɗi da ke cike da matakai na tsake bakin aljihu ya zo a daidai lokacin da ake cikin hali na matsi amma nan gaba za a ga alfanunsa.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi