1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain za ta sami tallafin ƙungiyar Tarrayar Turai

June 25, 2012

A karon farko Spain ta baiyana aniyarta a hukumce ga ƙungiyar Tarrayar Turai ta samin rance domin ceto bankunanta

https://p.dw.com/p/15LFY
A man is seen reflected in the glass building of the Bankia bank headquarters in Madrid, Wednesday May 9, 2012. New bank president Jose Ignacio Goirigolzarri took over the troubled bank Wednesday after former conservative economy minister for Spain and former managing director for the International Monetary Fund, Rodrigo Rato resigned. Prime Minister Mariano Rajoy dodged a question on whether the government planned to nationalize troubled lender Bankia, Spain's fourth-largest bank and the most exposed to bad loans on real estate. (Foto:Paul White/AP/dapd).
Hoto: dapd

Ƙasar Spain ta buƙaci samun agaji a hukumce ga ƙungiyar Tarrayar Turai na kuɗin da za a bata rance domin ceto bankunanta dake cikin halin durkushewar tattalin arziki.

Ko da shi ke ƙasar ba ta fayace addadin kuɗaɗen da ta ke so ba ,amma a makonnin biyun da suka gabata hukumomin na Spain,sun sanar da cewar suna buƙatar biliyan dubu 62 domin ceto bankunan,dangane da wannan sanarwa da ƙasar ta bayana, yanzu haka kuɗin ruwa ya ƙaru a kuɗaɗen basusukan ƙasar, yayin da kasuwannin hanayen jari na ƙasar suka yi ƙasa da kashi ukku.Gwamnatin ta Spain ta ce za ta fara tattaunawa da ƙungiyar Tarrayar Turan akan yawan kuɗaɗen rance da za a bata da kuma ƙaidoji da za a giciya mata kafin taron ƙungiyar ƙasashen Tarrayar Turai da za a gudanar a ƙarshen wannan wata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Auwal