Spain: Zaben gama gari na majalisar dokoki
April 28, 2019Talla
Jam'iyyar Sanchez ta Socialist Workers Party da ke kankankan da jam'iyyar adawa, na bukatar hadin kan kanana jam'iyyu don kafa sabuwar gwamnati, idan damar ta kubuce mata to akwai yiwuwar masu ra'ayin rikau karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Party su za su samar da gwamnatin hadaka wadda za tga hada da Vox party ta masu matsanancin ra'ayin rikau wadda ke zama sabuwar jam'iyya a fagen siyasar kasar.
Kimanin 'yan kasar miliyan 37 suka cancanci kada kuri'a a zaben da ya kasance irinsa na uku da Spain ke gudanarwa a cikin shekaru hudu.