1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SDP ta lashe kujerar gwamna a Niedersachsen

January 21, 2013

Jam'iyar Social Democrat ta Jamus ta lashe kujerar gwamna a jihar Niedersachsen ko Lower Saxony a zaben da ke zama gwajin dafi ga zaben tarayya a watan satumba.

https://p.dw.com/p/17OHY
Sabon gwamna Stephan Weil na SPD ya nuna doki bayan lashe zabe.Hoto: picture-alliance/dpa

Kujera daya tilo ta majalisar jiha kawance jam'iyun adawa na SPD da kuma The Greens ya tsere wa bangaren jam'iyun CDU da kuma FDP da ke rike da mulkin Niedersachsen ko Lower Saxony. Hasali ma dai bangaren jam'iyun da ke rike da madafun iko sun tashi ne da kashi 45,9% na kuri'un da aka kada, yayin da wadanda suka kalubalance su wato SPD da kuma The Greens suka lashe kashi 46,3 na kuri'un. Wannan jihar dai ita ce ta biyar da ta kubuce wa jam'iyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tun bayan fara wa'adin mulkinta na biyu a shekara ta 2009, baya ga Hambourg da Baden Württemberg da NordRhein Westfalen da kuma Schleswig-Holstein.

Tasirin da SDP za ta yi a daya daga majalisun Jamus

Tuni dai dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus karkashin Social Demokrat wato Peer Steinbrück ya danganta nasarar da jam'iyarsa ta samu da wani sharan fage na zaben tarraya da zai gudana a watan satumba mai zuwa idan Allah ya yarda. Farin jininsa dai ya ragu a makwanin baya-bayannan sakamakon subul da baka da ya yi ta yi. Steinbrück wanda tsohon ministan kudi ne ya ce nasarar SPD a jihar Niedersachsen na nunawa cewa jam'iyar SPD za ta yi kai labari cikin watanni takwas masu zuwa.

Niedersachsen/ Der Kanzlerkandidat der SPD, Peer Steinbrueck, steht am Samstag (19.01.13) in Goettingen beim Strassenwahlkampf der SPD fuer die Landtagswahl 2013 in Niedersachsen vor roten Luftballons. Die Wahl findet am Sonntag (20.01.13) statt. Foto: Swen Pfoertner/dapd
Steinbrück na SPD ya yi imanin cewar zai iya doke Merkel na CDU a satumba.Hoto: dapd

"Wannan na nufin cewar a wannan shekarar akwai yiwuwar canjin gwamnati musammam lokacin da za a gudanar da zaben watan satumba. "

ita dai Jam'iyar ta SPD ta kuma lashe akasarin kujerun da aka ware wa Niedersachsen ko Lower Saxony a majalisar jihohi ta Bundesrat. Wannan ya na nufin cewa ta samu karfin adawa da duk daftarorin doka da gwamnati za ta mika wa majalisar tare da shigar da wannan ta ke ga ya fi dacewa. Wannan halin dai zai haddasa tafiyar hawainiya a fannin dokoki ko da jam'iyar CDU ta Merkel ta samu rinjaye a majalisar wakilai ta Bundestag bayan zaben watan satumba mai zuwa.

Daya daga cikin wadanda  ba su ji da dadi ba a wannan zabe na jihar Niedersachsen  ko Lower Saxony shi ne gwamna mai barin gado David McAllister na CDU. Dalili kuwa shi ne a lokacin da tauraransa suka haska a yakin neman zabe, an danganta shi da daya daga cikin wadanda za su iya maye gurbin Angela Merkel nan gaba. Masharhanta na ganin cewar kashin kaji da tsohon gwamnan wannan jiha kana tsohon shugaban kasa Christian Wulff  ke fama da shi, ya shafi Jam'iyar CDU da kuma dan takararta.

Niedersachsen/ Niedersachsens Ministerpraesident David McAllister (CDU) winkt am Sonntag (20.01.13) in Bad Bederkesa beim Gang vom Wahllokal nach Hause. Am Sonntag wird in Niedersachsen ein neuer Landtag gewaehlt. (zu dapd-Text)
Mulki ya kubuce wa McAllister na CDU a jihar Lower saxony.Hoto: dapd

Linke ta tashi a tutar babu yayin da FDP ta samu ci gaba

Sai dai kuma akwai wasu jam'iyu da ba su lashe ko da kujera guda a zaben na jihar Niedersachsen ko Lower Saxony ba. daga cikinsu kuwa har da Linke da ke da ra'ayin rikau da kuma Piraten da ke da ra'ayin cire shinge da ake sanyawa a kafar sadarwa ta internet. Sai dai kuma a daya hannun Jam'iyar FDP da ke kawance da CDU ta Angela Merkel ta ba wa marada kunya a zaben Niedersachsen ko Lower Saxony inda ta lashe kashi 10%  na kuri'un da aka kada. Ita dai wannan jam'iya na fuskantar wasu matsaloli na cikin gida. Lamarin da daya daga cikin kusoshinta wannan ba wani ba ne illa dai Dirl Niebel, ministan raya kasashe masu tasowa ya ce ya zama wajibi a gudanar da babban taro  domin gano hanyoyin farfado da martabarta.

Amma kuma shugaban jam'iyar ta FDP Philip Rösler ya ce ci gaban da ta samu ya ba ta damar bude wani sabon babi na tarihinta.

Landtagswahlen Niedersachsen 2013 Wahlurne Wähler Deutschland Rösler
Rösler da Jam'iyarsa ta FDP sun samu ci gaba a Niedersachsen.Hoto: ODD ANDERSEN/AFP/Getty Images

"Na buga wa Stefan Birkner waya a Hannover. Lallai fa wannan babbar rana ce ga FDP a jihar Niedersachsen. sannan kuma in atabbatar muku cewa rana ce ta musamman ga 'yan FDP da ma dai 'ya liberal a Tarrayar Jamus baki daya."

Al'amura da suka taka rawa a zaben na Niedersachsen ko Lower Saxony dai sun hada da batun ilimi da kuma tattalin arziki.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: mohammad Nasiru Awal