SPD za ta fidda dan takara a watan Janairu
November 21, 2016Jam'iyyar SPD da ke cikin gwamnatin kawancen Jamus ta ce a farkon shekarar 2017 za ta yanke shawara game da wanda za ta tsayar takarar nemen mukamin shugaban gwamnatin Jamus. Majiyoyin jam'iyyar a birnin Berlin sun nuna cewa a gun babban taron manyan shugabanninta a karshen watan Janerun 2017 za a tsayar da dan takarar. Shugabanta Sigmar Gabriel da shugaban majalisar dokokin Turai Martin Schulz ke kan gaba a jerin 'yan takarar. Da farko Firimiyar jihar North-Rhein Westfalia, Hannelore Kraft 'yar jam'iyyar SPD, ta ce za su yi aiki cikin tsanaki.
Ta ce: "Social Democrat jam'iyya ce mai ji da kanta. Tsarin lokacinta bai dogara kan lokacin da CDU da CSU suka tsayar da dan takara ba. A saboda haka za mu tattauna da juna cikin tsanaki, kun san dokokinmu ba bu kuma abinda ya canja a ciki."
A wannan Lahadi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, 'yar jam'iyyar CDU, wadda tun a shekarar 2005 ke rike da wannan mukami ta ce za ta sake yin takara karo na hudu a jere.